Gwamnatin Tarayya Ta Baiwa Kowanne Gwamna Naira Biliyan 30 – Akpabio

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio yace gwamnatin tarayya ta bai wa kowannne gwamnan jiha naira biliyan 30 domin amfani da su wajen ragewa talakawa radadin tsadar rayuwar da suke fuskanta.

Akpabio ya bayyana haka ne lokacin zaman majalisar tarayyar, a ci gaba da tattauna irin halin kuncin da jama’ar kasar suka samu kan su a ciki, wanda ake dangantawa da cire tallafin mai.

Shugaban majalisar yace ya samu wadannan bayanai ne daga wajen hukumar tara kudaden haraji ta kasa da ake kira ‘Internal Revenue Services’ wadda ta mikawa jihohin wadannan kudaden da ake Magana a kan su.

Akpabio yace wadannan kudade sun saba da naira biliyan bib-biyu da aka bai wa gwamnonin daga cikin biliyan biyar-biyar na rancen samarwa jama’ar su tallafin rage radadin cire tallafin man fetur.

Shugaban majalisar ya bai wa gwamnonin shawara wajen yin amfani da wadannan makudan kudade ta hanyar da ta dace domin ganin jama’ar jihohin su sun samu tallafin da ya dace, musamman abinda ya shafi abinci.

Akpabio yace ana iya cimma nasarar gabatar da tallafin ne ta hanyar amfani da shugabannin kananan hukumomi saboda kusancin su da mutanen dake yankunan karkara.

Shugaban majalisar wanda ya yi watsi da zanga zangar da aka gani a wasu jihohin kasar da ake danganta su da tsadar rayuwa, ya zargi ‘yan adawa da daukar nauyin su, duk da kokarin da yace majalisar dattawan na yi domin tinkarar matsalar tare da gwamnatin tarayya.

Akpabio yace babu wani mahaifin dake fatar ganin ‘dan sa ya kwanta ba tare da ya ci abinci ba, saboda haka ya bukaci takwarorin sa da su mayar da hankali a kan daukar matakin samo abinci duk inda yake domin wadata jama’a.

Yanzu haka ‘yan Najeriya na ci gaba da cacakar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan yanayin da kasar ta samu kan ta, na hauhawan farashin kayan masarufi da kuma tsadar rayuwa, saboda abinda suka kira rashin shugabanci na gari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories