Gwamnatin Binuwai Ta Ba Wa Makiyaya Wa’addin Ficewa Daga Faɗin Jihar

Gwamnatin jihar Binuwai ta umarci makiyayan da ta ce sun shigo jihar suna kiwon dabbobinsu a fili su gaggauta ficewa su koma inda suka fito.

Kwamitin tsaro na jihar karkashi jogarncin Gwamna Hyacinth Alia, ya kuma gargadi wadanda yake zargi sun gayyato makiyayan da su gaggauta daina hakan ko su fuskanci fushin hukuma.

Majalisar tsaron ta umarci sarakunan gargajiya da sauran jama’a da su kai rahoto ga hukumomin tsaro domin hukunta masu hada baki ko gayyatar makiyayan zuwa jihar.

Har ila yau, ta ba da wa’adin kwanaki 14 ga makiyayan da suke kiwon dabbobinsu a fili a jihar da su daina ko kuma su kuka da kansu.

Taron majalisar tsaron ya ce dole makiyaya su bi dokar hana kiwo a fili a jihar, tare da jaddada cewa har yanzu dokar tana aiki.

Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke Makurdi a daren Talata, sakataren yada labaran gwamnan, Tersoo Kula, ya ce majalisar ta kafa kwamiti mai mutum bakwai don tabbatar da aiwatar da wa’adin da aka ba wa masu karya dokar daga ranar Laraba, Fabrairu. 21 ga Disamba, 2024.

Majalisar ta bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu su kuma kula da harkokin tsaro domin gwamnatin na kokarin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Jihar Binuwa na daga cikin jihohin arewa ta tsakiya a Najeriya da rikicin makiyaya da manoma ya daidaita, a sama da shekaru goma. Dokar hana kiwo a fili da gwamnatin jihar ta kafa ta kara ta’azzara rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories