Zanga-zanga Kan Matsin Rayuwa A Najeriya: Ba Gudu Ba Ja Da Baya – NLC

Kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC ta bayyana cewa “babu gudu ba ja da baya” game da gudanar da zanga zangar da ta shirya yi na kwanaki biyu daga ranar 27 zuwa 28 na wannan wata da muke ciki na Feburairu a fadin kasar.

Shugaban kungiyar Comrade Joe Ajero ne ya bayyana hakan a matsayin martani ga gargadin da hukumar tsaron ‘yan sandan farin kaya ta kasar “DSS” ta yi musu kan gudanar da zanga-zangar,kamar yadda jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta ruwaito.

Tun da farko, hukumar tsaron ta ‘yan sandan sirri, ta gargadi shugabancin kungiyar kwadagon da takwaransa na TUC kan cewa su janye zanga zangar da suke shirin yi domin barazana ce ga tsaron kasar.

Sai dai a martaninsa ga hukumar, Shugaban NLC Ajero, ya ce “tarihi ba zai yafe wa kungiyoyin kwadagon ba, idan har suka zuba ido halin matsin rayuwa da al’umma ke ciki ya ci gaba, wanda ya faru ne sakamakon abin da ya kira da “mulkin rashin tausayi” na gwamnatin Najeriya da mukarrabanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories