Dambarwar Hisbah A Kano: Yadda Sheikh Aminu Daurawa Ya Fitar Da Malamai Kunya

Hikimar shiga malamai gwamnati shi ne domin su taimaka wajen samar da nagarta da kuma dakile barna. Idan ya zama shugaba zai fito duniya ya gwasale wannan aikin to ci gaba da zama a ciki zubar da darajar malanta ne da kuma yarda da daukakar fajirai.

Idan Mallam Aminu ya ci gaba da zama, duk da wannan wulakancin da aka yi wa aikin da yake yi, to kimar malanta za ta zube, kuma abinda za a yi masa da duk wani malami sai ya fi wannan. Za a zarge shi da kwadayi, za a yi wasa da mutuncin sa. Idan aka yi haka to an samar da sabon ma’aunin mu’amala da malamai a cikin gwamnati. Duk malami mutuncin sa a haka za a dauke shi a cikin gwamnati.

Babban abinda ya fi birge ni kuma shi ne Malam ya da fitar da mu kunya, ya yi abin da ba a saba ba. Ya yi abinda wadanda ba malamai ba suka kasa yi. Ya nuna sanin manufa da sanin kimar kansa da kuma uwa uba fifita kare addini a kan wani status na duniya.

Amma ‘yan duniya sai a yi ta yiwa mutum wulakanci yana nane.

Aiki ne ja wur a kan malamai su dada kaimi wajen karfafawa musulmi riko da addini da kuma fifita dokar Allah a kan komai. Dole a dada saita tunanin mutane a kan ganin girman Allah da jin haushin abinda Allah ba ya so.

Ta haka al’umma zata kara riko da addini sosai da girmama sha’anin Allah, wannan zai saka ko ba don Allah ba shugabanni su hau layi.

Mahmud Muhammad ya rubuto daga Kano – Najeriya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories