Gwamnatin Buhari Ce Silar Haifar Da Hauhawar Farashi A Najeriya — Gwamnatin Tarayya

Ministan Kuɗi da Gudanar da Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ɗora alhakin hauhawar farashin da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu a kan tsohuwar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.

Minista Edun ya ce buga takardun kuɗi na tiriliyoyin naira da Gwamnatin Buhari ta riƙa yi tsawon shekaru takwas ba tare samun wani kyakkyawan tasiri kan hakan ba shi ya haddasa matsalar da ƙasar ta tsinci kanta na matsalar tattalin arziki a yanzu.

Ministan kudi na wannan jawabi ne a gaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Dattawa a jiya Laraba.

A cewar Ministan, za su bi diddigin yadda Gwamnatin Buhari ta riƙa buga takardun kuɗi har na naira tiriliyan 22.7 da duk wata manufa da ke tattare da hakan.

Ya ce “Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta bai wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) umarnin buga takardun kuɗi har naira tiriliyan 22.7 a bisa tsarin da ake kira ‘Ways and Means’.

“Wannan tsari da Gwamnatin Buhari ta yi amfani da shi tun daga shekarar 2015 zuwa 2023 shi ya jefa Nijeriya cikin matsanancin yanayi na hauhawar farashi,” a cewar Ministan.

Ana iya tuna cewa dai Gwamnatin Buhari ta yi amfani da wani tsari da CBN ya kira ‘Ways and Means’ da ya riƙa samar mata da kuɗaɗen toshe gibin da aka samu a kasafin kuɗinta.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Kuɗin na Majalisar Dattawa, Sanata Sani Musa, ya ce za su ci gaba da gudanar da ire-iren wannan zama domin bijiro da hanyoyin da za a dakile matsalar tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories