Shugaba Tinubu Ya Naɗa Umar Abdullahi Ganduje Muƙami

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Umar Abdullahi Umar, ɗan tsohon Gwamnan Kano kuma Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ɗaya daga cikin manyan daraktocin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA).

Wannan ya zo bayan, “wani sabon bincike da aka yi kan yadda aka kashe kudaden hukumar,” kamar yadda sanarwar da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar an mata take da “shugaba Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar kula da samar da wutar lantarki daga aiki da shi da tawagarsa.”

Baya ga Shugaban, Tinubu ya dakatar da Olaniyi Netufo da Barka Sajou Sa’adatu Balgore.

Tinubu ya ba da umarnin a faɗaɗa bincike kan jami’an hukumar kan zargin “kashe wasu kudade da suka kai naira biliyan 1.2 cikin shekaru biyu ba bisa ƙa’ida ba, wanda tuni hukumar hana yi wa ƙasa ta’annati ta ƙwato wasu,” kamar yadda sanarwar ta ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories