Sojoji Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) sun yi nasarar daƙile wani yunkurin yin garkuwa da wasu mutane 10 da ƴan bindiga su ka yi ƙoƙarin yi a garin Tsafe da ke jihar Zamfara a jiya Talata.

 A cewar jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Suleiman Omale, a wata sanarwa da ya fitar a Gusau a yau Laraba,ya ce sojojin ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka yi nasarar daƙile harin.

 “Mun sami kiran gaggawa a daren ranar 12 ga watan Maris, 2024 inda sojoji suka dira garin tare da farwa ƴan bindigan.

 “Jajircewa, ya sa sojojin yin nasara akan ƴan bindigar inda suka gudu kowanne su da raunuka tare da barin waɗanda suka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories