Gwamnatin Adamawa Ta Bada Umurnin Rufe Makarantu Saboda Cutar Ƙyanda

Gwamnatin jihar Adamawa ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da ma masu zaman kansu da ke faɗin jihar sakamakon ɓarkewar cutar kyanda.

 Dama dai Makarantun gwamnati na shirin komawa zango na uku na shekarar 2023/2024. A ranar 6 ga watan Mayu.

 A Wata takardar da babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi, Aisha M. Umar ta sanya wa hannu ta ce “Dama An sanya 6 ga Watan Mayu, 2024 a matsayin ranar komawa makaranta amma sakamakon ɓarkewar cutar ƙyanda an maida 13 ga Mayu, 2024 a matsayin ranar komawa.

 Saboda haka an umurci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar da su rufe makarantun saboda wannan lamarin.

A cewar sakatariyar ta ce an rufe makarantun ne domin daƙile yaɗuwar cutar da kuma baiwa hukumar kula da lafiya matakin farko ta jiha (PHCDA) damar yi wa ƙananan yara allurar rigakafi.

 In ba Manta ba Wikkitimes ta ruwaito yadda cutar ƙyanda ta kashe mutane 42 a kananan hukumomi biyu na jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories