An rage kudin wutar lantarki

Kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki dake fadin kasar nan da suka hada dana Abuja da kewaye (AEDC) sun fitar da sanarwar yin ragin kudin wutar lantarki ga kwastomominsu dake kan rukunin samar da wuta na ‘Band A’.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wasu kamfanonin raba hasken wutar lantarki suka fitar a yau, Litinin, 6 ga watan Mayu.

A cikin watan Afrilu ne gwamnatin tarayya ta sanar da yin karin kudin wuta ga masu amfani da wutar lantarki rukunin ‘Band A’.

A cewar gwamnati, masu amfani da wutar lantarki dake kan rukunin ‘Band A’ suna samun wutar lantarki ta akalla sa’a 20 a kowacce rana.

Ma'aikatan wuta

Sanarwar Karin kudin wutar tazo ne a daidai lokacin da farashin kayan amfani ke hauhawa wanda hakan ya jawo barkewar cece-kuce a tsakanin ‘yan Najeriya.

DUWA WANNAN: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi
A sanarwar AEDC, wacce WikkiTimes Hausa taci karo da ita a dandalin sada zumunta na ‘X’, kanfamin ya CE ya rage kudin wutar daga N225/kWh zuwa N206.80kWh.

AEDC ya kara da cewa ragin kudin wutar ya fara aiki nan take daga yau Litinin, 6 ga watan Mayu, 2024.

Kazalika, kamfanin ya kara da cewa ragin kudin wutar bai shafi sauran kwastomimi dake kan rukunin ‘Band B’, ‘Band C’, ‘Band D’ da ‘Band E’ ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories