‘Ku kama shi’: Kotu tayi watsi da bukatar Yahaya Bello

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja tayi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ta neman kotu ta hana hukumar EFCC kama shi.

Kotun, a karkashin Jastis Emeka Nwite, ta bayyana Yahaya Bello a matsayin wanda ba ya biyayya ga umarnin kotu.

Kazalika, Jastis Nwite ya soki Yahaya Bello akan neman kotu ta hana a kama shi bayan ya ki amincewa ya bayyana a gabanta.

Alkalin ya bayyana cewa bukatar Yahaya Bello daidai take da neman hana hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu.

Tunda fari hukumar EFCC tana fatan gurfanar da Yahaya Bello akan tuhuma 19 da suka hada da cin amana, barnatarwa tare da karkatar da kudin jihar Kogi da yawansu ya kai biliyan N80. 2.

Tun a ranar 17 ga watan Afrilu EFCC ta samu izinin kotu domin kama Yahaya Bello tare da gurfanar da shi.

DUBA WANNAN: Bashin $350m: Majalisar Jihar Kaduna ta fara binciken El-Rufai

Amma a ranar 18 da ya kamata a gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu sai ya bijirewa jami’an EFCC da suka je kama shi.

Lauyan Yahaya Bello, Abdulwahab Mohammed, ya shaidawa Jastis Nweti cewa karamar kotu ce ta bawa EFCC izinin kama Yahaya Bello wanda hakan ba huruminta bane.

Adeola Adedipe, wani lauya daga cikin lauyoyin Yahaya Bello, ya sanar da kotun cewa Wanda suke wakilta yana fargabar bayyana a gaban kotu ne saboda kar daga nan a tsare shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories