Peter Obi ya ziyarci Atiku, Sule Lamido, da Saraki

Dan takarar neman shugabancin kasa a zaben 2023 a karkashin inuwar jam'iyyar LP (Labour Party), Peter Obi, ya Kai wata ziyarar bazata ga wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar PDP da suka fito daga arewa.

Dan takarar neman shugabancin kasa a zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar LP (Labour Party), Peter Obi, ya Kai wata ziyarar bazata ga wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar PDP da suka fito daga yankin arewa.

Obi ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, kafin ziyarar da ya kaiwa Atiku Abubakar a ranar Litinin.

Sanarwar ziyarar da Obi din ya kai tana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na kwamitin sadarwarsa, Yunusa Tanko, ya fitar a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, Obi ya kai wannan ziyara ne a kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya da cigaban kasa.

”Obi mutum ne da ya sadaukar da kansa domin samar da Najeriya da zata amfani dukkan ‘yan kasa tare da fitar dasu daga kangin fatara da talauci,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

DUBA WANNAN: ‘Annabawa ma sun je’: Hadi Sirika ya rarrashi ‘Yarsa a zauren kotu

“A dukkan wadanan ziyara da Obi ya Kai ya tattauna dasu ne akan halin da kasa take ciki da kuma yadda za a ragewa jama’a wahalhalun da suke ciki a ko ina a fadin kasar nan, “.

“Sannan ya nuna matukar kulawa da damuwarsa akan halin da arewacin Najeriya ke ciki, ” a cewar sanarwar.

Kafin ficewarsa daga jam’iyyar PDP, gabanin zaben 2023, Obi mamba ne a jam’iyyar PDP kuma shine wanda ya yi takara tare da Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben 2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories