Tinubu ya haramta siyen motoci masu amfani da fetur

A yayin zaman malisar zartarwa ta kasa (FEC) a ranar Litinin, Tinubu ya jaddada cewa babu gudu balle ja da baya wajen ganin sun kawo canji a bangaren makamashin da ababen hawa ke amfani da su.

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya haramtawa fulogan gwamnatinsa siyen motoci masu amfani da man fetur.

Kazalika, shugaban ya bada umarnin a gaggauta siyo motoci masu amfani da makamashin gas samfurin CNG (Compressed Natural Gas) ga ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.

Wannan sabon umarni yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ajuri Ngelale, mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai da sadarwa, ya fitar a ranar Litinin.

A cewar Ngelale, wannan sabon umarni yana daga cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na ragewa jama’a da direbobi wahalhalun da suka shiga sakamakon tsadar man fetur.

A yayin zaman malisar zartarwa ta kasa (FEC) a ranar Litinin, Tinubu ya jaddada cewa babu gudu balle ja da baya wajen ganin sun kawo canji a bangaren makamashin da ababen hawa ke amfani da su.

DUBA WANNAN: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

A cewar Ngelale, shugaba Tinubu ya ki amincewa da bukatun ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya na siyen motoci masu amfani da fetur.

Tun bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2023 shugaba Tinubu ya alkawarta cewa gwamnatinsa zata siyo motoci masu amfani da gas.

Kazalika, ya yi alkawarin cewa za a samar da kayan aiki da cibiyoyi domin sauya motoci masu amafani da fetur zuwa masu amfani da gas din CNG.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories