Kano: Mutumin da ya cinnawa Masallaci wuta ana tsaka da Sallah ya shiga hannu

A ƙalla masallata 20 ne a wani shahararren masallaci a garin Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano, suka samu raunuka daban-daban, sakamakon wani harin takife da aka kai da sanyin safiyar ranar Laraba, 15 ga watan Mayu.

Shaidun gani da ido sun ce wanda ake zargin ya zuba man fetur tare da cinna wuta a masallacin.

An tattaro cewa kimanin masallata 40 ne a cikin masallacin lokacin da lamarin ya faru. Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce “lamarin ya haifar da tashin hankali a yankin a safiyar ranar Laraba.

“Mutumin ya yi amfani da fetur ne ya cinna wuta a yayin da mutane kusan 40 daga cikinmu ke addu’a. Sannan ya garƙame masallacin bayan tada gobarar,” inji shi.

“An ɗauki lokaci kafin mutanen da ke waje su fahimci abin da ke wakana tare da ƙoƙarin kuɓutar da wadanda abin ya shafa yayin da suke yunƙurin ɓalle ƙofar masallacin don ceton rayukansu.”


An garzaya da masu ibadar waɗanda rahotanni suka tabbatar sun samu munanan raunuka zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke ƙwaryar birnin Kano.

KARANTA: HISBAH ta kama matasa 20 maza da mata saboda yin wanka tare a Kano

Sai dai, da yammacin ranar Laraba din ne babban jami’in ‘yan sanda, AIG Umar Mamman, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da sanar da cafke wanda ya kai harin.

AIG Umar ya tabbatar da cewa daya daga cikin mutanen da aka garzaya dasu asibiti ya rasu.

Kazalika, ya bayyana cewa wanda ya kai harin bashi da alaka da wata kungiyar ‘yan ta’adda.

A cewar AIG Umar, wanda ya kai harin ya yi hakan ne saboda nuna fushinsa akan rabon gado kamar yadda bincike ya fara bankadowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories