Ta’addanci: Rundunar sojin Najeriya tana neman Halilu Buzu dan Nijar ruwa a jallo

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa tana neman Halilu Buzu dan kasar Nijar ruwa a jallo saboda aiyukan ta’addanci a Najeriya.

Darekta mai kula da sadarwa a rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, shine ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

A cewar Manjo Janar Buba, Halilu ya shigo Najeriya tare da kafa sansani a dajin Subbubu dake karkashin yankin karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Ya Kara da cewa Halilu Buzu ya mallaki wani haramtaccen wurin hakar ma’adanai a Kawayi dake karkashin karamar hukumar Anka kuma yana da yara da yawa da suke yi masa aiki.

A cewar Manjo Buba, Halilu Buzu yana da hannu a aiyukan ta’addanci a jihar Zamfara da suka hada har da satar shanu.

Rundunar sojin ta kara da cewa ko a makon da ya gabata sai da yaran Halilu Buzu suka hallaka mutane 19 a kauyen Farar Kasa.

KARANTA: Sambisa: Sojoji sun hallaka shugaban kungiyar Boko Haram da ya gaji Shekau

“Babban dan ta’adda ne kuma muna nemansa ruwa a jallo.

“Sannan ya kasance mai safarar makamai da ‘yan ta’adda suka yarda da shi saboda yana shigo da makamansa tun daga Libiya.

”Mun dade muna bibiyarsa amma duk lokacin da muka kusa cimmasa sai ya tsallaka iyaka zuwa kasarsa Nijar ya buya.

“A wannan gabar ne muke kira ga hukumomin kasar Nijar da su bamu hadin kai da goyon baya domin ganin mun kama shi tare da gurfanar da shi,” a cewar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories