Zan bincika yadda Sarki Sanusi II ya koma kujerarsa amma ni babu hannu na – Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ko kadan babu saka hannunsa a mayar da Sanusi Lamido Sanusi kan kujerar sarkin Kano.

Kwankwaso ne ya fara nada Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 14 a shekarar 2014 kafin daga bisani Abdullahi Umar Ganduje ya tube shi a shekarar 2020.

Amma bayan jam’iyyar NNPP ta karbi mulkin Kano a shekarar 2023, Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatinsu za ta waiwayi maganar tube Sanusi II.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar Kano ta warware gyaran dokar masarautu da ta yi a shekarar 2019 gabanin tube Sanusi wanda hakan ne ya share hanyar dawowarsa kan kujerar sarkin Kano a karo na biyu.

Sai dai, a wata hira da BBC Hausa ta yi da Kwankwaso ya bayyana cewa babu hannunsa a abubuwan da suka faru har zuwa mayar da Sanusi II amma zai bincika dukkan abinda ya faru tunda zai shiga Kano.

”Zan shiga Kano kuma zan yi magana da gwamna, shugaban majalisa da wasu daga cikin mambobin majalisa domin sanin hakikanin abinda ya faru”, a cewar Kwankwaso.

KARANTA: HISBAH ta kama matasa 20 maza da mata saboda yin wanka tare a Kano

Kazalika, Kwankwaso ya bayyana cewa suna aiki tare da gwamna amma su aikinsu bayar da shawara ne kuma ba dole duk abinda gwamnati za ta yi sai sun saka hannu ba.

A cewar Kwankwaso, babu komai tsakaninsa da gwamnati sai fatan alheri da yi wa gwamnatin addu’a domin ta yi abinda ya dace wanda ba sai lallai shine zai tsara yadda za a gudanar ba.

Tuni rahotannin da WikkiTimes Hausa ta samu suka tabbatar da cewa Sanata Kwankwaso ya isa Kano kuma sarki Sanusi II ya koma matsayinsa na sarkin dunkulalliyar masarautar Kano mai cikakken iko duk a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories