Kano: Kotu ta umarci ‘yan sanda su fitar da Aminu Ado Bayero daga gidan sarki na Nasarawa

Wata babbar kotun Jihar Kano a karkashin jagorancin mai sharia Aisha Adamu Aliyu ta bawa ‘yan sanda umarnin su karbe iko tare da fitar da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, daga gidan sarkin Kano na Nasarawa inda yake zaman fada.

A hukuncin da kotun ta zartar a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu, Jastis Aisha ta haramtawa dukkan wani mutum gabatar da kansa a matsayin sarki a daya daga cikin masarautun Kano da aka rushe wadanda suka hada da Kano, Bichi, Rano, Karaye, da kuma Gaya.

Kazalika, hukuncin kotun ya umarci kwamishinan ‘yan sanda ya karbi iko tare da fitar da Aminu Ado Bayero daga cikin gidan sarkin Kano dake kan titin zuwa gidan gwamnati dake karamar hukumar Nasarawa har zuwa lokacin sauraronm karar da aka shigar ranar 24 ga watan Mayu.

Kotun ta dakatar da Aminu Ado daga gabatar da kansa a matsayin sarkin Kano.

DUBA WANNAN: ‘Babu wanda yafi karfin doka’ – Aminu Ado ya magantu kan dambarwar sarautar Kano

Tun cikin makon da ya gabata aka fara dambarwa akan sarautar Kano biyo bayan dokar da gwamnatin Kano ta zartar na rushe masarautu guda biyar na jihar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da dokar rushe masarautu biyar tare da dawo da sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi, a matsayin sarki daya tilo na dunkulalliyar masarautar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories