Majalisar dattijai ta zartar da kudirin canja taken Najeriya

Kudirin, wanda aka gaggauta amincewa da shi, bayan tsallake karatu na daya da na biyu a ranar Alhamis din makon jiya, yana jiran amincewar shugaban kasa, Bola Tinubu, kafin ya zama doka.

Majalisar dattijai ta zartar da kudurin canja taken Najeriya na shekarar 2024 wanda ya amince da komawa tsohon taken Najeriya da ake farawa da ‘’Najeriya, muna jinjina gare ki’’.

Kudirin, wanda aka gaggauta amincewa da shi, bayan tsallake karatu na daya da na biyu a ranar Alhamis din makon jiya, yana jiran amincewar shugaban kasa, Bola Tinubu, kafin ya zama doka.

Toshon taken Najeriya da majalisar ta amince a koma amfani da shi an kirkire shi ne a ranar 1 ga watan Oktoba na 1960 bayan samun ‘yancin Najeriya.

Sabon kudirn majalisar yana son a dawo da tsohon taken da aka daina amfani da shi a shekarar 1978 lokacin mulkin soja na tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

DUBA WANNAN: Dan majalisar wakilai daga jihar Abia ya Musulunta, ya sauya sunansa

Wani baturen kasar Ingila mai suna Jean William shine wanda ya rubuta taken yayin zamansa a Najeriya.

Tsohon taken ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo hadin kai da kaunar kasa a tsakanin shekarun 1960s zuwa karshen 1970s.

Jagoran majalisar dattijai, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa, “taken da za a koma amfani da shi zai dasa kishin kasa a tsakanin ‘yan Najeriya. Wadanda suka yi rayuwa a wancan lokacin zasu iya tuna irin tasirin da taken ya yi”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories