Kaduna: Mutane da dama sun rasu sakamakon harin ‘yan bindiga a kasuwa

Mutane da dama sun rasa ransu sakamakon wani hari da ‘yan b indigo suka kai kasuwar kwanar Maro da ke mazabar Maro a yankin karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna.

Kajuru na daga cikin yankin jihar Kaduna da ‘yan bindiga suke yawan kai hari.

Da take tabbatar da kai harin, rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta sanar da cewa mutane biyar sun samu raunuka a yayin da mutum daya ya rasa ransa.

Sai dai, mazauna yankin sun sanar da manema labarai cewa a kalla mutane 12 ‘yan bindigar suka kasha sakamakon harin ‘yan bindigar, kamar yadda Channels Television ta rawaito.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari kasuwar da misalign karfe 4:30 na yammacin ranar Laraba tare da bude wuta kan jama’a ta kowanne bangare.

Ya bayyana cewa mutane biyar sun samu raunuka daban-daban a yayin da wani mutum guda ya rasa ransa tare da bayyana cewa rundunar ‘yan sanda na cigaba da gudanar da bincike domin tabbatar da yawan adadin  mutanen da suka mutu.

KARANTA: Bashin $350m: Majalisar Jihar Kaduna ta fara binciken El-Rufai

A cewar Kakakin, jami’an rundunar ‘yan sanda da sauran tawagar jami’an tsaro sun garzaya zuwa kasuwar bayan samun kiran gaggawa tare da bayyana cewa yanzu haka suna bin sahun ‘yan bindigar domin kama su.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kawo harin ne daga dajin Kanwa na karamar hukumar Kajuru inda daya daga cikin sansaninsu yake,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories