Sarki Sanusi II Ya Yi Naɗin Sarauta Na Farko Bayan Mayar Da Shi Gadon Mulki

A Yayin da ake ci gaba da dambarwar rikici a Masarautar Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi naɗin sarauta na farko a yau alhamis.

Naɗin ya zo ne a kasa da makonni biyu bayan da kace-nace ta ɓalle game da kujerar sarautar Kano wacce gwamnatin jihar Kano ta mayar wa da Sanusi Lamido Sanusi.

Wanda aka naɗa Alhaji Hamisu Sani an naɗa shi ne a matsayin Mai unguwar ƙofar Mazugal da ke karkashin karamar hukumar Dala a cikin kwaryar birnin Kano.

Bayan naɗin Alhaji Hamisu, Sarki Sanusi II ya yi kira ga sabon Mai Unguwar da ya tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar yankin tare da bayar da gudunmawa wajen kawo cigaba a yankinsa da jihar Kano.

A ranar Alhamis, kafin nadin sarautar, hakimai da wakilan kungiyoyin ‘yan kasuwa da na addini sun kai wa Sarki Sanusi II ziyarar nuna goyon baya gare shi.

Daga cikin kungiyoin da suka ziyarci sarki Sanusi II akwai wakilan kungiyar Ansaruldeen ta mabiya darikar Tijjaniya da wakilan ‘yan kasuwar kantin kwari da kasuwar singa duk a cikin birnin Kano.

KARANTA: Abinda Sarki Sanusi II ya fadawa shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawarsu

A ranar Alhamis din makon jiya ne majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da kudirin rushe masarautun Kano guda biyar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira.

A ranar Juma’a ta makon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu a kan kudirin wanda hakan ke nufin ya zama doka a jihar Kano.

Bayan amincewa da dokar Abba ya sanar da dawo da sarki Sanusi II kan gadon masarautar Kano a matsayin sarki daya tilo, lamarin da har yanzu ke cigaba da yamutsa hazo a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories