Abinda Ribadu da Abbba suka tattauna yayin ganawarsu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci  mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, domin gabatar da neman afuwa akan zarginsa da hannu a dambarwar masarautar Kano.

A makon da ya gabata ne mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu abdulsalam, ya bayyanan cewa Ribadu ya umarci sojoji da wasu sauran jami’an tsaro su mayar da Aminu Ado Bayero gidan sarki bayan gwamnati ta tube shi.

Sai dai, Ribadu ya musanta wannan zargi tare da yin barazanar cewa zai maka Aminu Abdulsalam a kotu.

Tuni Aminu Abdulsalam ya fito ya nemi afuwar Ribadu tare da janye kalamansa.

Abba ya nemi afuwar Ribadu yayin ganwar sirri da suka yi a ofishinsa dake Abuja ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Gwamna Abba ya tube Aminu Ado Bayero daga sarkin Kano tare da maye gurbinsa da Sanusi Lamido Sanusi bayan zartar da dokar rushe masarautun jihar guda biyar.

Duk da sanar da tube shi, Aminu Ado ya dawo Kano bisa rakiyar jami’an tsaro tare da kafa wata fada ta daban a gidan sarki dake Nasarawa bayan kokarinsa na komawa fadar sarki bai samu ba.

KARANTA: Abinda Sarki Sanusi II ya fadawa shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawarsu

Al’amura sun yi zafin da har ya kai ga gwamna Abba ya bawa ‘yan sanda umarnin su kama Aminu Ado saboda kawo hargitsi a jihar Kano.

Sunusi Bature Dawakin Tofa, mai Magana da yawun Abba, ya shaidawa manema labarai cewa Abba ya bawa Ribadu hakuri baki da baki a kan zarginsa da hannu a rikicin masarautar Kano.

Kazalika, ya bayyana cewa Abba da Ribadu sun shafe fiye da sa’a guda suna tattauna a kan batutuwan da suka shafi dambarwar masarautar Kano da kuma sauran sha’anin tsaro da suka shafi jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories