NLC ta sanar da shiga yajin aikin ‘sai baba ta gani’

Hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da takwararta ta ‘yan kasuwa (TUC) ta sanar da shiga yajin aikin ‘sai baba ta gani’ daga ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2024, saboda gazawar gwamnati na amincewa da mafi karancin albashi da kuma karin farashin wutar lantarki.

Shugban kungiyar TUC, Festus Osifo, shine ya sanar da hakan ranar Juma’a yayin wani taron hadin gwuiwa da shugabancin NLC a birnin tarayya, Abuja.

A cewar shugabannin kungiyar kwadagon, sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin ne biyo bayan karewar wa’adin da suka bawa gwamnati na samar da matsaya a kan mafi karancin albashi kafin karshen watan Mayu.

“A saboda haka, mu, kungiyar kwadago (NLC) da TUC, muna sanar da fara yi wa gwamnatin tarayya yajin aikin sai baba ta gani,” a cewar Osifo.

A kwanakin baya ne WikkiTimes Hausa ta wallafa cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta fice babu shiri daga tattaunawa da gwamnati akan maganar Karin albashin ma’aikata.

KARANTA: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

Ana tattaunawar ne a tsakanin kingiyar kwadago da gwamnatin da kuma bangaren hadakar kungiyar ma’aikata a masana’antu.

Kungiyar kwadago ta fice daga tattaunawar ne bayan gwamnati ta kafe akan mayar da mafi karancin albashi zuwa N48, 000 kafin daga bisani ta tirje a kan N60,000.

Sai dai, NLC ta bayyana tayin da gwamnati ta yi a matsayin abin dariya Kuma abin wasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories