Dalilai 14 da FG ta bayar kan dagewarta akan mafi karancin albashi na N60,000

Gwamnatin Tarayya da Kungiyar ƙwadago a ranar Juma’a, 31 ga Mayu sun kasa cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.

Gwamnatin tarayya ta ƙara Naira 3,000 a farkon tayin N57,000 da ta gabatar a makon jiya, inda adadin ya kai N60,000 yayin da kungiyar kwadago ta rage bukatar ta ta hanyar cire N3,000 daga N497,000 da ta gabatar a makon jiya.

Gwamnati ta kare kanta bisa ganin baikenta da ake yi kan tayin N60,000.00 da suka yi a watan Mayu.

Ga dalilai 14 da gwamnatin tarayya ta bayar kan dagewarta akan mafi karancin albashi na Naira N60,000:

1. Biyan N35,000 na tsawon wata shida ga duk ma’aikatan tarayya a matsayin tallafin rage radadi

2. Naira biliyan 100 don siyan motocin bas masu amfani da wutar lantarki da gas CNG da aikin sauya motoci zuwa masu amfani da CNG.

    3. Naira biliyan 125 tallafi da bada bashi ga masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i (MSME) .

    4. Ware Naira 25,000 da za a raba wa gidaje miliyan 15 na tsawon watanni uku.

    5. Naira biliyan 185 (rance ga Jihohi) don rage tasirin cire tallafin man fetur.

    KARANTA: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

    6. Naira biliyan 200 don tallafawa noman hatsi tare bunkasa noman abinci.

    7. Naira biliyan 75 domin karfafa bangaren masana’antu.

    8. Ware Naira Tiriliyan 1 ga lamunin dalibai don neman ilimi mai zurfi.

    9. Sakin metric ton 42,000 na hatsi daga ma’ajiyar abinci ta ƙasa.

    10. Siye tare da rarraba metric ton 60,000 na shinkafa daga ƙungiyar masu sarrafa shinkafa ta ƙasa zuwa ga mabuƙata.

    11. Karin albashi na baya-bayan nan na kashi 25-35% akan dukkan tsarin albashin ma’aikatan tarayya.

    12. Kashi 90% na tallafin kiwon lafiya ga Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da aka yiwa rajista akan tsarin inshora ta NHIS.

    13. An ƙaddamar da layin dogo mai sauki a Abuja don rage farashin sufuri har zuwa karshen shekara. Tuni jihar Legas ta fara cin gajiyar wannan shiri da layinsu na Blue and Red.

    14. Baya ga ƴancin ma’aikatan gwamnati na yin noma, Gwamnatin Tarayya ta amince da shigar da ayyukan ICT (kimiyyar da fasahar zamani) da kuma wasu hanyoyin domin samun ƙarin kudaden shiga.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here

    This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

    Most Read

    Latest stories