Amarya ta yi yunkurin gutsure al’aurar ango yana bacci a Kaduna

Wata amarya mai suna Habiba Ibrahim ta yi yunkurin yanke al’aurar mijinta mai suna Salisu Idris yayin da yake tsaka da sharbar bacci a garin Kudan dake jihar Kaduna. Jaridar Daily Trusta ta rawaito cewa lamarin ya faru ne ranar 26 ga watan Mayu, 2024.

Salisu, mai sana’ar acaba, ya shaidawa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiya yayin da ya koma bacci bayan dawowa daga sallar asuba.

Ya bayyana cewa matarsa ta fado kansa rike da wuka mai kaifi inda gada-gadan ta fara yunkurin yanke masa al’aura.

Ya kara da cewa ba don makwabta sun kawo masa agajin gaggawa ba bayan ya yi ihu da Habiba ta cire al’aurarsa gaba daya.

Yanzu haka amarya Habiba tana hannun jami’an rundunar ‘yan sanda.

Salisu ya ce aurensa da Habiba bai wuce wata hudu ba tare da bayyana cewa har yanzu bai san dalilin da yasa ta yi yunkurin raba shi da al’aurarsa ba saboda sun yi auren soyayya kuma babu wani sabani da ya shiga tsakaninsu kafin faruwar hakan.

Daily Trust ta rawaito cewa an garzaya da Salisu zuwa asibitin garin Kudan kafin daga baya a mayar da shi zuwa babban asibiti dake Makarfi. Daga bisani an mayar da shi asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria inda likitoci ke kokarin ceto rayuwarsa.

DUBA WANNAN: Kaduna: Mutane da dama sun rasu sakamakon harin ‘yan bindiga a kasuwa

Mahifiyar Salisu ta shaidawa Daily Trust cewa duk da ba gida daya suke zaune da ma’auratan ba, Salisu bai taba yi mata korafi a kan amaryarsa ba.

“Iyayenta sun nuna damuwarsu matuka kuma sun nuna niyyarsu ta son daukar nauyin biyan kudin kula da shi a asibiti,” a cewar mahaifiyar Salisu.

Daily Trust bata samu nasarar yin Magana da likitocin dake kula da Salisu ba. Kazalika, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, bai samu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories