Sojoji sun kashe kasurgumin dan ta’adda Buharin Yadi a Katsina

Sojojin Najeriya sun hallaka wani ɗan ta’adda mai suna Buharin Yadi, ɗaya daga cikin ƙasurguman ‘yan bindiga da ake zargin sun addabi al’umma da ta’addanci a Arewacin Najeriya cikin shekaru goma da suka gabata.

Kwamishinan harkokin Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, dakarun rundunar ‘Sector 6 Operation Whirl Punch’ sun yi luguden wuta a kan sarkin daji da aka fi sani da Buhari Alhaji Halidu (wanda aka fi sani da Buharin Yadi) tare da ‘yan tawagarsa, inda aka kawo ƙarshen ta’addancin su.

“An kashe Halidu ne a wani ƙazamin gwabzawa tsakanin sojoji da ƴan-ta’addan (a karkashin jagorancin kwamandan su, da kuma babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya, Manjo Janar MLD Saraso) wanda ya gudana a kusa da dajin Idasu da ke kan iyaka tsakanin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna da karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, sojoji sun samu nasarar yin galaba akan ƴan-ta’addan bayan fafata bata kashi tsakanin su, inji shi”.

Aruwan ya ce sojojin sun fara aikin ne a sirrance a matsayin martani ga rahotannin sirri kan motsin ‘yan ta’adda daga Samunaka da ke yankin Saulawa a jihar Katsina.

Ya kara da cewa, “a lokacin da sojojin suka doshi garin Samunaka, sun gano wurin da aka lalata tare da kashe shanu, lamarin da ke nuna cewa ‘yan fashin daji sun aikata muggan laifuka a baya-bayan nan.

“Mummunan faɗa ya biyo baya cikin sauri, yayin da ‘yan ta’addan da ke gabatowa aka yi musu luguden wuta a Hayin Almajiri. Daga nan ne sojojin suka yi artabu ta hanyar kwanton ɓauna, domin cimma manufarsu.

“Ƙididdigar farko ta nuna cewa an kawar da aƙalla ƴan fashin daji 36 a cikin wannan samamen da suka kai.“

KARANTA: Borno: Rundunar soji ta kama soja da alburusai da gurneti boye cikin buhun shinkafa

“Buharin Yadi ya na da hannu dumu-dumu cikin manyan laifuka wadanda suka haɗa da satar shanu, garkuwa da mutane, ciniki da safarar makamai, ƙwamushe, da safarar miyagun kwayoyi.

“Ya jagoranci ’yan kungiyarsa wajen sace-sacen al’umma, kisan ƙare dangi da yanka dubbanin mutane a jihar Kaduna da jihohin da ke makwabtaka da su,”.

A cewarsa, wannan ƙasurgumin dan ta’adda maras tausayi da imani yana da alaƙa da sauran kungiyoyin ta’addanci da ke kashe mutane a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories