Yajin aikin KEDCO: Za a iya yin Sallah cikin duhu a Kano, Jigawa, Katsina

Jigawa, Kano, da Katsina sun shiga cikin matsalar rashin wutar lantarki a ranar Alhamis bayan ma’aikatan kamfanin raba hasken wutar lantarki na Kano (KEDCO) sun fara yajin aiki tare rufe babban ofishinsu na Kano da na sauran jihohin da suke bawa wutar lantarki.

Mataimakin babban sakataren kungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki (SSAEAC) shiyyar arewa, Dakta Baba Gana, ya bukaci dukkan ma’aikatan KEDCO su shiga yajin aiki har sai sun samu biyan bukatunsu.

BabaGana ya yi kira ga uwar kungiyar ma’aikan wutar lantarki a kasa (NUEE) ta basu goyon baya a yajin aikin da suka fara da safiyar ranar Alhamis.

A cewar BabaGana, sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne biyo bayan gazawar KEDCO wajen inganta yanayin aiki kamar yadda suka amince a wata yarjejeniya da suka kulla.

Ma'aikatan wuta

Ya bayyana cewa mahukuntan KEDCO sun ki mayar da kudin fansho na wata 79 da suka cire daga albashin ma’aikata tare da kin mayar da wasu kudi da aka dinga yanka daga albashin ma’aikata har na tsawon wata 80.

KARANTA: Ranar Dimokradiyya: Muhimman Sakonni 8 Daga Jawabin Tinubu

Har ila yau, ya ce har yanzu KEDCO ta gaza biyan bashin albashi na wata daya da ake bawa ma’aikatan KEDCO a karshen kowacce shekara a matsayin cikamako na wata 13 a shekarar 2019, 2022, da 2023.

Kazalika, Babagana ya ce KEDCO ta ki mayar da hankali wajen inganta sauran ofisohinta a jihohin da take rarraba hasken wutar lantarki tare da kin samarwa da ma’aikata kayan aiki lamarin da ya ce ya saka ma’aikata yin aiki cikin hatsari.

BabaGana ya bayyana cewa zasu cigaba da yajin aikin har zuwa lokacin da mahukunta a KEDCO suka biya musu bukatunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories