Muna Duba Yiwuwar Saka Dokar Ta Baci A Kan Barkewar Annobar Kwalara – NCDC

Babban darekta a cibiya dakile yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC), Dakta Jide Idris, ya bayyana cewa suna duna yiwuwar saka dokar ta baci a kan cutar kwalara matukar annobar ta cigaba da mamaya a fadin kasa.

Dakta Olajide ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da yake gabatar da jawabi a wurin taro da wata kungiyar kwararru a bangaren lafiya ta shirya a Victoria Islanda da ke jihar Legas.

Ya bayyana cewa yanzu haka suna jiran alkaluma na adadin mutanen da cutar ta kama daga wurin jami’ansu da suka tura domin tattara bayanai a kan yaduwar annobar.

“Idan alkaluma suka nuna cewa annobar ta kai wani mataki, to dole mu saka dokar ta baci a kan lamarin,” a cewar Dakta Olajide. Ya kara da cewa har yanzu suna jiran rahoto daga tawagar kwararru da ke gudanar da bincike.

DUBA WANNAN: Kano: Abba ya rattaba hannu kan sabuwar dokar ‘gwaji dole’ kafin aure

Tuni rahotanni suka bayyana cewa annobar cutar kwalara mai haddasa amai da gudawa ta bulla a jihohi 30 na Najeriya, lamarin da yasa hukumar lafiya ta duniya (WHO) da sauran takwarorinta suka kira wani taron gaggawa a Legas ranar Talata.

A wani rahoto na baya bayan nan da NCDC ta fitar, ta ce an samu rahoton samun mutum 1,141 da suka kamu da cutar Kwalara tare da tabbatar da kamuwar mutum 65 da mutuwar mutane 30 bayan bullar annobar a kananan hukumomi 96 a jihohi 36.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories