Dakarun Soji Sun Kashe Gawurtaccen Shugaban ‘Yan Bindiga Kachalla Ragas A Kaduna

Dakarun rundunar soji sun samu nasarar kashe gawurtaccen shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Ragas, tare da wasu sauran ‘yan ta’adda yayin wasu tagwayen hari da sojoji suka kai karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

A wani jawabi da kwamishinan harkokin tsaron cikin gida a jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce harin da dakarun rundunar ‘Whirl Punch’ suka kai ta sama da kasa ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan bindiga da dama da shugabanninsu a yayin da suka hadu a wani wurin taronsu da ke cikin dajin Yadi a karamar hukumar Giwa.

“Kamar yadda rahoto ya samu gwamnatin jihar Kaduna, dakarun soji sun kai harin bayan samun sahihan bayanan sirri wanda har ya kai ga an samu nasarar shugabannin ‘yan bindiga a iyakar Kaduna da Katsina.

“Sahihan bayanai sun nuna cewa ‘yan bindiga zasu hadu a wani wurin taronsu domin tattauna yadda zasu kawo mummmunan hari a kauyukan da ke daura da dajin Yadi.

“Sojoji sun sahun ‘yan bindigar tare da tabbatar da bayanan da suka samu, sun ga ‘yan bindigar dauke da makamai yayin da suke tunkarar wurin taron su a kan babura.

DUBA WANNAN: Masu kwacen waya sun kashe hazikin babban soja a Kaduna

“Bayan sun tabbatar da hakan, sun kai hari kan ‘yan ta’addar tare da kashe da dama daga cikinsu da suka hada da Alhaji Kachalla Ragas – abokin yarintar tsohon shugaban ‘yan bindiga da aka kashe, Buharin Yadi,” a cewar Aruwan.

Aruwan ya kara da cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ji dadin samun labarin kashe ‘yan ta’addar tare da jinjinawa kokarin sojoji da kuma yabawa wadanda suka bayar da bayanan sirri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories