Gwamnatin Sokoto na shirin tsige Sarkin Musulmi – MURIC

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta koka kan shirin da Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato ya ke yi na tsige Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

 Babban Darakta na MURIC, Farfesa Isiaq Akintola Shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Sai dai ana ganin cewar ba a gama da rikicin Kano ba game da tsige Sarkin da Gwamnan Kano Abba Gida – Gida yayi ba.

 In ba a manta ba a baya dai Gwamna Aliyu ya kori sarakunan gargajiya 15 bisa wasu laifuka daban – daban.

“ Majiya ta bayyana cewa daga yanzu zuwa ko wani lokaci gwamnan Sokoto na iya tsige Sarkin Musulmi ta hanyar amfani da duk wasu uzuri da aka yi amfani da su wajen tsige sarakunan gargajiya 15 da ya yi a kwanakin baya .

 “MURIC ta shawarci gwamna da ya dubi dakyau kafin yanke hukunci.  Kujerar Sarkin Musulmi bakwai kawai kujerar gargajiya bace hadda ma addini. Haka kuma ikon kujerar ba iya Sokoto kawai ta tsaya ba Ya shafi Najeriya baki ɗaya. Shi ne shugaban ruhin dukkan musulmin Nijeriya.

 “Saboda haka duk gwamnan da ya yi yinƙurin wasa da kujerar sarkin Musulmi  to Musulmin Najeriya za su killace shi domin Sarkin Musulmi ya hada ofishin Sarkin Musulmi da na Shugaban NSCIA,” in ji Akintola.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories