Tsohon Hoton Matashi Lokacin NYSC Ya Jawo Masa Goma Ta Arziki

Wani tsohon hoto na wani matashi, Umar Ibrahim Umar, lokacin da ya ke bautar kasa (NYSC) ya jawo masa goma ta arziki daga wurin jama’a.

Ya zuwa wannan lokaci, jama’a sun tattara kudin da yawansu ya kai N300,000 domin bawa Umar tallafi ya samu jari domin fara sana’ar harkar kudi ta POS.

Yunkurin tallafawa Umar ya yadu tare da samun karbuwa a dandalin sada zumunta har ta kai ga tsohon ministan sadarwa, Isah Ali Pantami, ya nuna niyyarsa ta bayar da tasa gudunmawar ga matashin.

A shekarar 2018 ne Umar ya zama abin tattaunawa wurin jama’a bayan wani hotonsa da aka dauka a sansanin horon masu bautar kasa da ke Wailo a jihar Bauchi ya mamaye dandalin sada zumunta.

An dauki hoton ne a daidai lokacin da Umar ya wage baki yana bayar da umarni ga sauran abokansa ‘yan bautar kasa yayin faretin kammala zaman sansanin bayar da horo (POP) a ranar 16 ga watan Agusta na shekarar 2018.

“Abokai da ‘yan uwa da dama sun kira ni washegari bayan fitar hoton domin sanar da ni cewa hotona ya yi farinjin a dandalin sada zumunta,” kamar yadda Umar ya sanar da WikkiTimes yayin ganawar su.

KARANTA: Sakamakon JAMB 2024: ‘Yar Jihar Bauchi ta yi bajinta

“Na ga wani ya saka hotona tare da fadin cewa; ‘ya kamata a biya wannan dan bautar kasa fiye da N19,800 da ake bawa sauran ‘yan bautar kasa.’ Hoton ya karada ko ina.”

Tun bayan lokacin, hukumar NYSC da sauran fitattun masu amfani da dandalin sada zumunta suka cigaba da amfani da hoton Umar domin manufa da dalilai daban daban.

“Mutane sun kalli hoton ta fuskoki daban-daban. Yayin da wasu suke amfani da hoton saboda na birge su, wasu kuma suna amfani da shi ne domin raha da zolaya,” kamar yadda Umar ya bayyana.

Wasu abokan Umar ne suka fara kawo tunanin cewa ya kamata jama’a su fara hada kudi domin a tallafa masa ganin yadda wasu suke amfani da hotonsa wajen samun kudin shiga.

KARANTA: Matashiya ‘yar shekara 33 ta zama alkaliya a babbar kotun jihar Jigawa

A nasa bangaren, Umar ya bayyana cewa, “kamar kimanin shekara biyu da suka gabata aka fara yada maganar cewa ina harkar POS. Da abokai na suka kawo shawarar a nemi jama’a su tara min kudi domin na fara sana’ar, sai naga lallai hakan wata dama ce da zata iya mayar da mafarki na ya zama gaske,” a cewar sa.

Tunanin a tattara wa Umar kudi ya samu karbuwa tare da yaduwa a dandalin sada zumunta daban-daban. Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, Umar ya tabbatar da cewa an tara masa kudin da yawansu ya kai N300,000 a matsayin tallafi daga wurin jama’a da suka hada da tsohon Minista Pantami.

“Wani mutum ya taba tuntuba ta domin karbar takarduna na neman aiki. Sannan, Farfesa Isa Ali Pantami ya nemi yin magana da ni,” kamar yadda Umar ya bayyana.

Umar ya nuna jin dadinsa tare da yin godiya ga duk wadanda suka bayar da tallafi domin ya fara harkar POS tare da bayyana cewa yanzu abinda ya rage kawai shine ya samu wuri mafi dacewa domin fara wannan kasuwanci na harkar POS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories