Jami’in EFCC Ya Kashe Kansa A Cikin Gidansa A Abuja

Wani jami’in hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ya kashe kansa a gidansa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

An bayyana marigayin, daya daga cikin sahun ma’aikata na biyar da aka dauka aiki a EFCC, a matsayin haziki kuma jajirtaccen ma’aikaci.

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa tuni an fara gudanar da bincike domin gano dalilin jami’in na kashe kansa.

Jami’an hukumar yaki da cin hanci, EFCC.

Jami’in ya kashe kansa ne ranar Litinin a gidansa. Ba a bayyana sunan jami’in ko wurin da gidansa yake ba a Abuja.

DUBA WANNAN: Ajali: Babban Jami’in Kwastan Ya Yanke Jiki Ya Fadi Babu Rai A Zauren Majalisar Wakilai

Wata majiya ta bayyana cewa alaka ta yi tsami tsakanin Marigayin da wata jami’a ta gaba da shi a hukumar EFCC a ‘yan kwanakin baya bayan nan.

Sai dai, babu tabbacin cewa ko hakan ne dalilin da yasa ya kashe kansa.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ba zata fitar da sunan jami’in ba saboda a halin yanzu ana gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories