An Kama Shugaban Jam’iyyar PDP Da Ake Zargi Da Safarar Makamai Zuwa Zamfara

Jami’an tsaron hadin guiwa sun ce sun yi nasarar kama wasu mutane uku da ake zargi da safarar makamai ga barayin daji a jihar Zamfara.

An gano cewa daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Aminu Ibrahim shi ne shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Birnin Yero ta karamar hukumar Shinkafin jihar.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa an kama mutanen ukun a ranar Litinin da ta gabata

Ƴan bindiga masu muggan makamai sun daɗe suna ta’adi a Najeriya musamman yankin arewa maso yammacin ƙasar, inda suke kashewa da yin garkuwa da dubban mutane – lamarin da ke haifar da fargaba ga matafiya da kuma hana yin noma a wasu yankuna.

Haka kuma jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar hare-haren ƴan bindiga ta yi ƙamari. Jihar kuma ta yi fama da rikicin siyasa, wanda wasu ke ganin yana tasiri ga ƙoƙarin shawo ƙarshen matsalar tsaron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories