Garba Shehu Ya Buƙaci Ƴan Najeriya Da Su Rage Buri Akan Gwamnatin Tinubu

Tsohon Mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu, ya buƙaci al’ummar Najeriya da su rage dogon buri akan gwamnatin Bola Tinubu.

Garba Shehu wanda ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a gurin taron tattaunawa ta musamman da kamfanin Media Trust kan gudanar a kowacce shekara a babban birnin tarayya Abuja.

“Toshon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shiga matsala ne kan yawan buri da ƴan Najeriya suka ɗora masa, wannan darasi ne da ya kamata mu koya.”

“Irin wannan dogon burin da tsammanin bai kamaci dan Adam ba, domin shugabanni za su yi abu da yawa amma ba komai ba.”

Ya ce ka da ƴan Najeriya su wuce gona da iri kamar yadda suka yi a tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Haka kuma Garba Shehu ya shawarci ƴan Najeriya da su rage domin buri ga gwamnatin Tinubu don samun abin da ake nema tare da koyar darasi kan abin da ya faru a gwamnatin baya don kada su saka rai kan abin da ba zai samu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories