Har Yanzu Atiku Yana Cikin Magagin Faɗuwa Zaɓe – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mayar wa babban mai hamayya da shi na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da martani bayan sukar gwamnatinsa.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jami’iyyar hamayya ta PDP a zaben da ya gabata, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya sauka daga shugabancin kasar idan ba zai iya shawo kan matsalolin tsaron da kasar ke fama da su ba.

Atiku Abubakar, wanda shugaba Tinubu ya kayar a zaben da ya gabata, ya zargi shugaban da yin wasa da aikinsa yayin da kasar ke nutsewa cikin matsalar tsaro da ta tabarbarewar tattalin arziki.

Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta yi watsi da kalaman na Atiku tana mai cewa wata suka ce irin ta ‘yan hamayya.

A sanarwar martani da ta fitar, fadar shugaba Bola Tinubu ta ce har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku.

“Mun san cewa har yanzu zafin shan kaye bai saki Atiku ba don haka zai iya furta komi na sukar shugaba Tinubu,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories