Harin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna,An Bankaɗo Waɗanda Suka Yi Maƙarƙashiya

Rundunar ƴan sanda ta sanar da cafke Ibrahim Abdullahi Mande ɗan bindigan da ya jagoranci kai harin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja 

 In ba a Manta ba a watan Maris din shekarar 2022 ne ƴan Bindiga suka kai hari kan titin jirgin ƙasa Abuja -Kaduna inda suka yi awon gaba da mutane da dama tare da kashe wasu.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewar  sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane sashen binciken manyan laifuka na jihar Kaduna (SCID) Su ne suka kama Mande a ranar 12 ga watan Janairun 2024.

 Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ACP Olumuyiwa Adejobi, wanda shi ne ya gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutane sama da 30 da aka kama da aikata laifuka daban-daban a jihar.

Jami’in ya ce tabbas Mande ya amsa cewa shi ne shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

“Mande yana cikin tawagar da suka jagoranci sace ɗaliban Jami’ar Green Field, kuma yana da hannu a kusan dukkanin garkuwa da mutane da ake yi a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories