Sambisa: Sojoji sun hallaka shugaban kungiyar Boko Haram da ya gaji Shekau

Bayan samun dumbin makamai a sansanin da aka kashe Tahir, an kashe wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram dake tare da shi a yayin da wasu suka gudu da raunukan harbi.

Rundunar soji ta ‘ofireshon Hadin Kai’ ta samu nasarar hallaka Tahir Baga, babban kwamanda a kungiyar Boko Haram da ake zaton shine ya gaji Shekau.

Rahotanni sun bayyana cewa Tahir ya kasance na hannun dama kuma waziri ga tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, marigayi Abubakar Shekau.

An Samu nasarar kashe Tahir ne a cigaba da kokarin rundunar soji na kakkabe sauran mayakan kungiyar Boko Haram a maboyarsu dake dajin Sambisa.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar majiyarta ta tabbatar mata da cewa an kashe Tahir ne a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.

Wata jarida, da ake kira Zagazola makama, mai wallafa rahotanni akan harkokin tsaro a yankin tekun Chadi ta tabbatar da kisan Tahir.

A cewar jaridar, an samu nasarar kashe Tahir ne bayan wasu manyan ‘yan kungiyar Boko Haram sun bawa rundunar tsaro hadin kai bayan sun shiga hannu.

Kisan Tahir ba kankanin koma baya bane ga al’amuran kungiyar Boko Haram.

”Tahir ya kasance makusanci ga Abubakar Shekau. Yana daga cikin wadanda suka fara kafa kungiyar Boko Haram a cikin Maiduguri kafin daga bisani su koma dajin Sambisa tare da irinsu Mamman Abarnawy, Kaka Ali, Abu Maryam, Mustapha Chad, Abu Kirimima da sauransu”.

DUBA WANNAN: Borno: Rundunar soji ta kama soja da alburusai da gurneti boye cikin buhun shinkafa

”Tahir Baga ya kasance daga cikin jagororin kungiyar Boko Haram kuma mai karfin fada a ji da ya yi amfani da mukaminsa wajen hana mayakan kungiyar Boko Haram mika wuya ga jami’an tsaro, ” a cewar wata majiya.

Majiyar ta kara da cewa Tahir ya kware wajen amfani da kananan yara mata wajen kai harin bam bayan ya yaudaresu da cewa zasu shiga aljanna idan sun mutu.

Bayan samun dumbin makamai a sansanin da aka kashe Tahir, an kashe wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram dake tare da shi a yayin da wasu suka gudu da raunukan harbi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories