HomeSiyasa

Siyasa

Don ‘yan Najeriya ne – Shettima yayi karin haske kan sabbin haraji

Halin da ƙasa ke ciki shine ya tilastawa gwamnati yin nazarin ja da baya domin gyara ɗamararta don gudun kada wankin hula ya kai ta zuwa dare.

‘Ku kama shi’: Kotu tayi watsi da bukatar Yahaya Bello

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja tayi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ta neman kotu ta hana hukumar EFCC kama shi.

Isa Dogon Yaro, mamba a majalisar wakilai, ya rigamu gidan gaskiya

Isa Dogon Yaro, mamba a majalisar wakilai ta kasa daga mazabar Babura da Garki a jihar Jigawa ya rasu a yau, Juma'a. Dogon Yaro, mai shekaru 46, ya rasu a Abuja bayan fama da gajeriyar jinya.

‘Annabawa ma sun je’: Hadi Sirika ya rarrashi ‘Yarsa a zauren kotu

Babbar kotun Abuja ta amince da bayar da belin Sirika tare da sauran wadanda aka gurfanar tare da shi akan N100m kowanne mutum tare da mutum biyu da zasu tsayawa kowa.

Badakalar N2.7b: EFCC zata gurfanar da tsohon minista Hadi Sirika tare da diyarsa

A cewar EFCC, za a gurfanar da Sirika, minista a gwamnatin tsohon shugaba Buhari, a gaban Mai shari'a, Sylvanus Oriji, na babbar kotu dake unguwar Maitama a Abuja.

Bashin $350m: Majalisar Jihar Kaduna ta fara binciken El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya sha korafin cewa jihar Kaduna bata da isassun kudin da zata gudanar da mulki saboda bashin da ake bin jihar.

Ziyarar Amurka: Kashim Shettima ya dawo Najeriya bayan samun matsalar jirgi

Sanarwar data gabata ta bayyana cewa Shettima ya bar Najeriya zuwa kasar Amurka domin halartar wani taron bunkasa kasuwancin kasashen Africa Wanda za a yi a birnin Dallas dake jihar Texas.

An rage kudin wutar lantarki

Kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki dake fadin kasar nan da suka hada dana Abuja da kewaye (AEDC) sun fitar da sanarwar yin ragin kudin wutar lantarki ga kwastomominsu dake kan rukunin samar da wuta na 'Band A'.

Most Read

Latest stories