Farashin Yankan Farce Ya Tashi A Kano

Ƙungiyar masu yankan farce ta ƙaramar hukumar Rano a jihar Kano ta sanar da ƙarin farashin yankan farce a jiya Lahadi.

Shugaban kungiyar Malam Adamu Rinji ne ya tabbatarwa da jaridar WikkiTimes cewa sun yi ƙarin farashin yankan farcen ne saboda yadda abubuwa su ka tashi.

Ya ce “mun yi ƙarin kuɗin ne sakamakon yadda abubuwan da mu ke amfani da su wajen wannan sana’ar su ka tashi”

“Kuɗar almakashi ta tashi haka ma farashin shi kan sa almakashin ga kuma uwa uba kuɗin motar da wasu daga cikin mambobin ƙungiyarmu su ke biya kafin su shiga cikin gari su gudanar da wannan sana’a”

Sabon farashin dai ya koma naira 150 a maimakon 100 sai kuma gyaran ƙafa naira da hannu inda kowanne ya koma naira 80.

A Najeriya dai al’umma na kokawa kan tsadar rayuwa da tashin farashin kayan abinci, lamarin dai ya yi ƙamarin da ya sa wasu daga cikin al’ummar ƙasar suka fara gudanar da zanga-zanga a wasu daga cikin jihohin kasar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories