Shekara Hudu da Hukumar Alhazan Jihar Zamfara Ta gaza Maidowa Alhazai 504 kudaden su

Hukumar alhazai ta jihar Zamfara a ranar Litinin din da ta gabata ta ce ta gano kimanin Naira miliyan 774 da ba a mayar wa maniyyata 504 da sukayi niyyar tafiya aikin hajj a shekarar 2019.

 Alhaji Musa Mallaha, shugaban hukumar shi ne ya bayyana haka a garinGusau a wajen taron kaddamar da hukumar.

 Sannan ya kara da cewa daga shekarar 2019 zuwa yau, gwamnatin da ta shude ba ta biya maniyyata 504 da suka ajiye kudaden su Naira miliyan 775 ba har yanzu.

 “Ana bin Hukumar alhazai bashin Naira miliyan 775 na maniyyata 504 daga kananan hukumomi 14 wadanda su ka kasa iya kammala biyan kudin kujerun aikin hajji su daga shekarar 2019 zuwa yau.

Mallaha wanda aka nada shi shugaban hukumar a wannan shekarar  ya bayana  cewa “Mutane da dama sun koka masa cewa sun yi ajiyan kudadensu a hukumar domin aikin hajji na tsawon shekaru amma har yanzu an kasa mayar musu da kudaden su.

 “Na kai kuka wa Gwamna, bayan da na karbi ragamar hukumar kuma Gwamna ya umarce ni da in binciki lamarin tare da tabbatar da yin adalci ga duk wanda aka rikewa kudi.

 “Sannan kuma Mun kara gano cewa hukumar na da asusun banki daban daban har guda 16 saboda haka na bukaci ofishin Akanta-Janar na jiha da ya tantance dukkan asusun banki bayan mun yi nasarar kwato Naira miliyan 254.

 “Mun kuma gano cewa wasu daga cikin kudaden da mahajjata suka ajiye an yi amfani da su ne wajen yin tikitin aikin hajji kyauta da kuma gyaran sansanin Alhazan jihar wanda gwamnatin da ta shude ta yi.”

 A cewarsa, a halin yanzu, hukumar ta na da kimanin Naira miliyan 92 daga cikin Naira miliyan 775 da za a biya.

 Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da gudanar da bincike kan kudaden tare da tabbatar da an yi adalci kan lamarin.

Saboda haka muna kira ga Gwamna Da yayi dubi ga wannan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories