Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Inuwa

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, a ranar Alhamis, ta tabbatar da nasarar da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar Gombe.

Kotun ta ce, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ta tabbatar da sahihanci da ingancin zaɓen gwamnan Inuwa ta yi daidai domin shi ne halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar. 

Kan hakan kotun ɗaukaka ƙarar ta kori ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takarar ta Jibrin Barde suka shigar da suka ƙalubalanci hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen na tabbatar da gwamna Inuwa na jam’iyyar APC. 

Idan za a tuna dai hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta shelanta cewa Gwamna Muhammad Yahaya shi ne ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da ƙuri’u 342,821.

Yayin da ta ce Muhammad Jibrin Barde na PDP ya samu ƙuri’u 233,131 a zaɓen da aka fafata a jihar. 

Amma Barde ya garza kotu domin ƙalubalantar nasarar Inuwa da iƙirarin cewa ba a bi dokar zabe ta 2022 ba wajen gudanar da zaɓen. 

Sai dai kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar mai Alkalai uku a ƙarƙashin Justice S.B. Belgore, ta kori ƙarar da cewa bai da inganci. 

Hakan ya sa ɗan takarar PDP ya sake garzayawa kotun ɗaukaka ƙara.

Kazalika, a ranar Alhamis ita ma kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar bisa cewa korin PDP bai da makama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories