Nakiya Ta Yi Ajalin Mutane 20 Da Jikkata 2 A Yobe

Daga Halima Lukman

Mutane 20 sun rasa rawukan bayan wani babur ya taka bam da ‘yan ta’addan Boko Haram suka dasa a jihar Yobe a yammacin ranar Talatar da ta gabata.

Nakiyar ta tashi ne da misalin karfe 6:30 na yamma a kauyen Goni Mittiri da ke garin Gumsa a karamar hukumar Gaidam a jihar, kamar yadda ganau suka shaida LEADERSHIP.

Wadanda lamarin ya rutsa da su, an ruwaito suna kan hanyarsu ta dawowa daga makabarta ne, bayan birne mutane 17 da Boko Haram suka kashe a safiyar ranar Litinin.

Wasu majiyoyi sun ce an dasa nakiyar ne a gefen hanya.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, “Mun kidaya jimillar mutane 20 a wurin da lamarin ya faru.”

Ya ce, sun yi jana’izar mamatan kamar yadda addini ya tanadar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories