An Kashe Mata, Yaro, Garkuwa Da Wasu Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Farmaƙi Zagayen Maulidi

Ana fargabar mutane da dama ciki har da mata da yaro ne aka kashe yayin da wasu kuma suka jikkata a wani harin da ‘yan fashin daji suka kai kan masu zagayen murnar zagayowar Maulidi a ƙauyen Musawa da ke jihar Katsina.

A ƙalla mutum 18 ne lamarin ya shafa inda aka kai wasu zuwa asibitin Orthopaedic da ke Katsina domin duba harsasan bindigogi, yayin da wasu kuma aka kai su zuwa babban asibitin Musawa.

‘Yan bindigan sun buɗe wa masu zagayen maulidin ruwan alburusai ne wajajen ƙarfe 10:05 na daren ranar Lahadi, inda a nan take suka yi garkuwa da wasu a wajen da suke buɗe wutan.

An tattaro cewa kafin jami’an tsaro su kawo ɗauki, ‘yan bindigan har sun gama cin karensu babu babbaka sun arce.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin ga ‘yan jarida, kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce, waɗanda lamarin ya shafa mutum 18 ne.

“An kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin musu jinya. Daga baya, biyu daga cikinsu sun rasu. 

“Ana cigaba da zurfafa bincike domin ganin an kamo waɗanda suka aikata hakan,” PPRO ya shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories