Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Fashin Daji 3 A Kaduna

Dakarun soji da ke ƙarƙashin 1 Mechanised Division da Operation Whirl Punch sun samu nasarar kashe wasu da ake zargin ‘yan garkuwa da mutane ne su uku a wani samamen kakkaɓe bata-gari da suka yi a ƙaramar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna.

A wata sanarwar da mai riƙon daraktan yaɗa labarai na bataliyar, Liyutanal Kanal Musa Yahaya, ya ce, sojojin a ranar Lahadi sun tsunduma wani aikin share ‘yan fashin daji a dajin Maro-Chibiya da ke ƙaramar hukumar Kajuru inda suka yi kicibus da ‘yan bindigan lamarin da ya kai su ga musayar wuta.

Ya ce, a nan ɗin sun kashe ɗan bindiga ɗaya, wasu ‘yan bindigan sun arci na kare da harbin bindigogi a jikinsu.

A cewarsa, sojojin sun samu nasarar kwato bindiga ƙirar AK-47, wata bindiga ƙirar gida, AK-47 da alburusai haɗi da wayar salula.

A cewarsa, “Sojojin sun kuma gudanar da irin wannan samanen a ƙauyukan Kwara da Filin Jalo da ke ƙaramar hukumar Igabi inda nan ma suka hallaka wani ɗan bindigan tare da kwato makamai da alburusai yayin da sauran su ma suka gudu da harbin bindiga a jikinsu.

“Haka-zalika, sojojin sun kuma aiwatar da sharan daji a Mai- Kulu- Gwanda, Rafin Gora, Funtua Badadi da Kabawa ƙauyukan da dukka suke ƙaramar hukumar Birnin Gwari, nan ma sun kashe wani ɗan bindigan da kamo abun magana na oba-oba da mashin na ‘yan bindiga.”

A cewarsa, kwamandan bataliyar 1 division, Manjo Janar Valentine Okoro, ya jinjina wa ƙoƙarin sojojin tare da nemansu da su ƙara zage damtse domin kakkaɓe ‘yan ta’adda a duk inda suke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories