Masarautar Gumel Ta Sake Fitar Da Sabbin Dokoki Sauƙaƙa Aure

Masarautar Gumel da ke karamar hukumar Gumel ta Jihar Jigawa ta fitar da wasu dokoki da ka’idoji da za a bi don ganin hidimar aure ya saukaka a yankin.

Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata takarda da ta fito daga Masarautar ta Gumel mai ɗauke da sanya hannun sakataren masarautar Alhaji Murtala Aliyu .

Inda takardar ta bayyana wasu dokoki guda goma sha tara da masarautar ta gindaya kan aure, tun daga kan akwati zuwa bikin aure da kuma daukar amarya.

Dokokin su ne kamar haka:

1. Ba a ƙayyade sadaki ba amma kar yafi karfin aljihu duba da yadda tattalin arziki yake a kasar.

2. Kayan akwati kuwa kar su wuce Tufafi Shida (6) .

3. Takalma kar su fi kafa uku (3).

4. Ɗan kunne da sarƙa uku (3).

5. Mayafi da hijabi suma uku (3).

6. Ɗankwali uku (3).

7. Kayan kwalliya kar su fi saiti biyu (2).

8.A jimmila dai ba a son kudin hada lefe ya wuce Naira Dubu Dari (100,000).

9.An soke mata su kai lefe sai Maza ne zasu riƙa kaiwa.

10. An hana biyan kuɗin na-gani-ina-so

11. Kudin sa rana ma an hana.

12. An hana yin gara.

13. An hana yin kaɗe-ƙaɗe da raye-raye domin hakan na jawo chakuduwar maza da mata.

14. Kada shagalin biki ya wuce daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.

15. Motoci uku (3)kawai aka yarda su kai amarya.

16. Kai amarya kada ya wuce karfe 6:00 na yamma.

17. An hana duk wani bidirin biki irin su ƙauyawa day, Arabian night, Yoruba night da sauran su.

18. An hana hawan angwanci sai an nemi izinin fadar masarautar Gumel.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories