An Hallaka Sufeto A Artabun ‘Yan Sanda Da Sojoji A Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, ta tabbatar da cewa, an kashe wani ɗan sandan mai muƙamin Sufeto, Jacob Daniel a yayin artabun da jami’ansu da sojoji suka yi a jihar a ranar Labara.

Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sandan jihar SP Suleiman Yahaya, shi ne ya tabbatar da hakan a yayin ganawa da ‘yan jarida a Yola.

SP Yahaya ya ce, lamarin ya faru ne sakamakon musayar wuta da ‘yan sandan suka yi da kuma mummunar harin da aka kai shalkwatar ‘yan sandan da ke jihar, inda Insfekta Daniel ya rasa ransa.

Kazalika, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya yi Allahwadai da rigimar da ta ɓarke tsakanin ‘yan sanda da sojojin.

Babalola ya umarci a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan lamarin da nufin wanzar da adalci da zaman lafiya a tsakani.

Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa koda wasa ba za su lamunci kai hari kan jami’an da ke bakin aikinsu ba.

Ya ƙara da cewa rayukan jami’ansu na da matuƙar muhimmanci don haka ba za su yi sako-sako a zubar musu da rayukan jami’ai ba.

Ya jaddada aniyar hukumar na yin aiki tuƙuru domin cigaba da kare rayuka da dukiyar al’umman jihar.

Ya nemi kowa da ya kwantar da hankalinsa yayin da shugabannin ɓangarorin tsaron suke kan yin duk mai yiyuwa domin shawo kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories