Masarautar Ningi Ta Warware Rawanin Salisu Zakari Daga Sarautar Ƙauran Ningi

Daga Sadam Mato Burra 

Masarautar Ningi ta cimma matsayar cire Hon. Salisu Zakari Ningi daga saraukar Ƙauran Ningi bisa sokar aikin kwangilar tagwayen hanya a ƙaramar hukumar Ningi. 

A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hanun sakataren fadar Sulaiman Shehu Burra, mai kwanan wata 17/11/2023, ta ce an sauƙe shi ne sakamakon rashin kishin Ningi da kuma ƙalubalantar aikin tagwayen hanya da gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya ƙaddamar kwanakin baya.

Idan za a iya tunawa Hon Salisu Zakari wanda tsohon ɗan majalissar tarayya ne da ya wakilci Ningi/Warji, ya ƙalubalanci kuɗin da aka ware don gudanar da aikin hanyar wato naira billiyan goma wanda hakan ya jawo cece kuce a tsakanin ‘ya’yan ƙaramar hukumar ta Ningi.

Da alamar kalaman Hon Zakari bai yi wa masarautar daɗi ba ganin yadda gwamnatotcin da suka shuɗe basu damu da cigaban garin ba sai wannnan gwamnatin ta Bala Abdulkadir Muhammad don haka ta ɗauki wannan mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories