La Liga na nazarin wani faifan bidiyo da aka nuna wariyar launin fata ga Vinicius Jr

La Liga na nazarin wani faifan bidiyo da aka ruwaito yana nuni da wariyar launin fata ga Vinicius Jr a wasan da Real Madrid ta buga a Valencia.

A wani Bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda wani yaro magoyin bayan Valencia ke cin zarafin dan wasan, a cewar rahoton The Athletic.

Vinicius ya zura kwallaye biyu a wasan da suka tashi 2-2 a ranar Asabar kuma ya yi murna ta hanyar daga hannu sama.

Dan wasan mai shekaru 23 ya fuskantar cin zarafi na wariyar launin fata a lokuta da dama a kasar ta Spain.

A cikin wata Mayu na shekarar 2023, Vinicius ya bayyana cewa “La Liga gas ace ta masu wariyar launin fata” bayan da magoya bayan Valencia suka zage shi a Mestalla.

Daga baya an kama wasu mutane uku da laifin cin zarafin dan wasan sannan aka ci tarar Valencia tare da umarnin rufe wani bangare na filin wasansu na wasanni biyar, daga baya aka mayar da shi uku bayan daukaka kara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories