Mata Na Da Kaso 31 A Nade-naden Mukamai Na Gwamna Bala

A nade-naden da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya yi mata sun tashi da kaso 31 cikin 100 na kaso na farko na mukaman siyasa da aka yi, kamar yadda wani bincike mai zaman kansa da WikkiTimes ta gudanar ya nuna.

Bincike ya nuna cewa kason ya yi ƙasa da tsarin mulki na ƙasa saboda bai kai kashi 35 cikin 100 da ake son bai wa mata ba a dukkanin mukaman gwamnati a Najeriya. Kodayake duk da haka wasu na yaba masa domin gwamnoni da dama ba su iya kawai haka ba.

Gwamnan ya yi nade-naden mukamai har kashi biyu jim kadan bayan fara wa’adin mulkinsa na biyu – kwamishinoni 24 da shugabannin kwamitocin riko 40 da mataimakansu.

A kowace karamar hukuma an nada kwamishina daya daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar domin kafa majalisar zartarwa ta jiha. Sannan an nada shugabannin kwamitocin riko da mataimakansu, wadanda su ne ke kula da yadda ake tafiyar da majalisun yankinsu kafin gudanar da zaben kananan hukumomi.

Mata sun sami kashi 21 cikin 100 na nadin kwamishinoni, ya zuwa yanzu mata biyar ne kawai gwamnan ya nada. Ya nada Tsammani Lydia Haruna a ma’aikatar ilimi mai zurfi da aka kirkiro; Hajara Jibrin Gidado mai kula da ma’aikatar harkokin mata da ci gaban yara;  Hajara Yakubu Wanka aka nada a sabuwar ma’aikatar jin kai, sai kuma Amina Mohammed Katagum da aka bai wa ma’aikatar filaye da safiyo da kuma Dr Jamila Mohammed Dahiru a ma’aikatar ilimi.

Hakazalika, a cikin shugabannin kwamitocin riko na kananan hukumomi 40 da mataimakansu, mata hudu ne kawai aka nada wanda hakan ya nuna suna wakiltar kashi 10 cikin 100. Nadin Dakta Zainab Baban Tako a matsayin shugabar karamar hukumar Bauchi yana daga cikin manyan mukamai da suka fito fili, su kuma sauran matan an nada su ne a matsayin mataimaka.

An nada Jamila Aliyu Adamu a matsayin mataimakiyar shugabar karamar hukumar Warji; Bahijja Baki mataimakiyar shugaba Giade da Tasalla Kawu Labaran mataimakiyar shugaban karamar hukumar Darazo.

Kungiyoyin kare hakkin mata da masu fafutuka na ci gaba da matsa kaimi wajen ganin an shigar da mata cikin harkokin siyasa da gudanar da mulki a Najeriya, inda suke bayyana cewa ya kamata ace mata suna da kashi mai tsoka a matakai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories