Ina Aka Kwana Kan Rage Farashin Simitin BUA?

Duk da doki da zumudin da al’ummar Nijeria suka yi a lokacin da shugaban Kamfanikn Simimtin BUA, Alhaji Rabiu AbdulSamad ya sanar da rage farashin simintin BUA zuwa naira 3, 500, bincike ya nuna cewa, har yanzu ‘yan kasuwa basu rage farashin ba, suna sayawa ne a kan tsohon farashin, wanda hakan bai yi wa mutane dadi ba.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne hukumar gudanarwa da kamfanikn simintin BUA ta sanar da ragin wannan da aka shirya zai fara aiki daga ranar 2 ga watan Oktoba 2023 amnma har zuwa yau babu inda suka rage farashin a fadin Nijeriya.

Mako daya bayan sanar da rage farashin amma manyan dillalan simintin sun bayyana cewa, har yanzu ba a sauko musu da farashin ba kamar yadda hukumar kamfanin ta sanar tun da farko.

Wani dillalin simintin a unguwar Isolo ta Jihar Legas, Alhaji Abioudun Haruna ya babayan cewa, a halin yanzu bashi da masaniya game da rage farashin simintin an hukumance.

Ya ce duku da cewa, har yanzu yana sayar da tsohon kayan da ya siya ne tun kwanakin baya, amma babu yadda zai sako da farashi a halin yanzu tun da umarnin bai zo daga kamfanin ne ba kaitsaye.

Ya ce, har yanzu ba a rage kudaden da ake kashewa wajen saffarwa tare da aikin fito da simintin da rarrabawa wurwre ba, ba a kuma rage kuadden wutar lantarki ba a kuma rage kudin man gas da motoci ke amfani da su wajen zirga-zirga da kayayyakin ba, to, ta yaya za a rage kudin siminti? kuma har a samu riba?.”

Alhaji Haruna ya kuma ce, a halin yanzu harkar saye da sayar da siminti babu riba saboda al’umma ba ta gine-gine suke yi ba, ta batun abinci al’umma kawai suke yi a halin yanzu.”

Haka kuma shugaban kamfanin Ajomobi & Co Enterprise, Eniola Ajomobi ya ce, duk da Kamfanin BUA ya sanar da rage farashi amma har yanzu kamfanin bai fara basu kaya a sabon farashin ba. Ya kara da cewa, suna fatan a nan gaba za su fara samun kayayyakin a kan sabon farashi don suma su sayar a kan farashin da kamfani da sanar.

Shi ma shugaban kamfanin Dominion Goshen da ke garin Lokoja, Asiwaju Dominion ya ce, yana kyau in har aka rage farashin siminti amma dai a halin yanzu farashin siminti na nan a yadda yake a kamfanin BUA, da na Dangote ba a rage ko sisi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories