Ranar Kwai Ta Duniya: Masu Kiwon Kaji A Najeriya Sun Nuna Damuwa Kan Tsadar Kayan Kiwo

Kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya (PAN), reshen jihar Legas, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta taimaka wa fannin wajen sassauta farashin kayyakin kiwo domin bunkasa noman Kwai a gida.

Shugaban kungiyar ta PAN a Legas, Mojeed Iyiola, wanda ya yi wannan kira a wata hira da manema labarai a gabanin gabannin shirye-shiryen ranar ƙwai ta duniya ta shekarar 2023, ya bayyana cewa nan gaba kadan masu kiwon kaji za su daina bikin wannan rana.

Ana bikin ranar kwai ta duniya kowace ranar Juma’a ta biyun kowace shekara a watan Oktoba.

Iyiola ya bayyana cewa saboda matsalolin da ake fuskanta a fannin, masu kiwon gida ba za su iya bin jerin sauran kasashen duniya ba wajen bikin ranar kwai ta duniya.

“Yayin da Ranar Kwai ta Duniya ke gabatowa, ba mu sani ba ko nan gaba za mu iya cigaba da wannan al’ada.

“Za a iya fuskantar karancin kwai saboda ƙarin kuɗin kayyaki da muke fuskanta.

“Ba ma iya kiwata yawan da muka saba yi a shekarun baya saboda matsalolin da ake fuskanta a fannin kiwo.

“Abu daya da za a iya mana din samun cigaba da wannan sana’a shi ne a saukaka mana tsadar kayayyaki ta fuskar abincin kaji.

“Muna kira ga gwamnati da ta ba mu a kungiyance lasisin shigo da masara da waken soya domin a samu saukin farashin kiwo a saukake” shugaban ya shaida wa NAN.

A cewarsa, waken soya da masara su ne manyan abubuwan da ke tattare da duk wani abinci kaji.

“Idan ba mu da wadannan abubuwan a cikin abincin, bayan mutuwar kaji har kwai ba za a samu a wurin kajin ba sosai.

“Muna son gwamnati a kowane mataki ta kawo mana agaji, yawanci wuraren kiwon kaji an rufe su. Bangaren kiwon kaji yana samar da ayyuka sosai ta fannin kiwo.

“In muka daina wanan kasuwanci, nan gaba kadan manoman kajin Najeriya ba za su iya bin sahun sauran kasashen duniya don bikin ranar kwai ta duniya ba,” in ji Iyiola.

Ya ce kungiyar za ta raba ƙwai kyauta ga mazauna shiyyoyin jihar.

“Kamar yadda al’ada ta tanada, za mu ba da ƙwai kyauta a duk faɗin yankunanmu, ga mazauna yankin a matsayin ba da gudummawa ga al’umma.

“Kodayake, ba za mu iya bayarwa kamar yadda muka saba rabawa a shekarun baya ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories