Mutum 5 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Tankar Mai A Kwara

Mutum biyar ne aka bada labarin sun kune kurmus har lahira da har ba a iya ganesu a ranar Asabar sakamakon wutar da ta barke daga wata motar tanka shake da man fetur a Kwara.

Majiyoyi sun ce wadanda suka rasun sun rasa rayukansu ne a hatsarin tankar da ya wakana a kan babban hanyar Illorin zuwa Jebba a karamar hukumar Moro da ke jihar.

Majiyoyin sun ce tankar ta fadi ne a kan hanyar lamarin da ya janyo hadarin.

Majiyar sun tabbatar da cewa mutum biyar ne suka rasa rayukansu yayin da wasu mutum bakwai kuma suka gamu da raunuka sakamakon hadarin na tankar man.

Da aka tuntubi jami’in watsa labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa jami’ansu sun yi kokarin kashe wutar gobarar.

“Mutane da dama sun jikkata wasu kuma daga baya sun rasu a asibiti. Amma ba zan iya baku adadin ba a halin yanzu,” Adekunle ya shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories